Mutane 200 sun jikkata a Bosnia

Masu zanga-zanga a Bosnia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga-zangar dai ta yadu a sassan kasar saboda batun rashin aikin yi da kuma cin hanci da rasahawa da ya yi katutu a kasar.

Jami'ai a kasar Bosnia sun ce kusan mutane dari biyu ne suka jikkata a tashin hankalin da aka yi a kasar a jiya juma'a.

An dai kona gine-ginen gwamnati a yawancin biranen kasar,'yan sanda sun yi amfani da harsashin roba da feshin ruwa akan masu zanga-zanga da suka lalata gine-ginen gwamnati da kokarin dunfarar fadar shugaban kasa a babban birnin kasar Sarajevo.

Zanga-zangar dai akan batun rashin aikin yi ne da kuma yadda cin hanci da rashawa ya yi katutu a kasar tun bayan kawo karshen yakin Bosnia shekaru ashirin da suka gabata.

Zanga-zangar dai ta yadu ne a farkon wanna makon da aka faro ta daga garin Tuzla, sanadiyyar rufe wata masana'antar tufafi.

Karin bayani