Yahudawa na son aurar junansu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yahudawa na kyamar dansu ya auri wacce ba Bayahudiya ba

Yahudawa na son auren junansu ne saboda gudun barazana ga al'ummar Yahudawa a duniya.

Wannan ne yasa Yahudawa a Isra'ila ke nuna rashin gamsuwar su da rahotannin dake cewa dan Firai-ministan Isra'ila yana neman aurar 'yan Norway.

Auratayya tsakanin masoya ( wato mace da namiji) masu tsatson al'ummomi daban-daban wata alaka ce da aka saba ganin tana kulluwa yau da kullum a sassa daban-daban na duniya.

To, amma a wajen wasu Yahudawa masu ra'ayin rikau, aure tsakanin Bayahude da wanda ba Bayahude ba, wata babbar barazana ce ga ci gaban rayuwar kasar Isra'ila.

Don haka ake tababa, shin me kenan zai faru yayin da wasu rahotanni ke cewa dan firaministan Isra'ila Benyamin Natanyahu yana neman wata yarinya 'yar asalin kasar Norway da aure?