Za a fara shari'ar Gimbiya Christina ta Spain

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masarautar Spain na fsukantar barazanar shari'a

A yau Asabar ne iyalan masarautar Spain zasu bayyana a gaban Kuliya a karon farko domin amsa tuhumar zamba.

Alkalin Mallorca ne zai yi wa Gimbiya Christina wadda ita ce karama cikin 'ya'yan sarki Juan Carlos tambayoyi game da yadda mijinta Inaki Urdangarin ya tafiyar da harkokin kasuwancinsa wanda ake zarginsa da yin al'mubazzaranci da miliyoyin dalolin gwamnati.

Sai dai dukansu sun musanta wannan tuhuma.

Shari'ar wacce aka dau lokaci anayinta, ta bata sunan Spain; ya kuma kawo illa ga goyon bayan da tsarin masarauta ke samu a kasar.

Karin bayani