A janye sojojin haya a Sudan ta kudu—Amurka

Image caption Rikicin Sudan ta kudu ka iya yaduwa a yankin

Amurka ta ya yi kira da a janye sojojin haya daga Sudan ta Kudu, tare da gargadin cewa hatsarin da ke cikin rikicin da ake tsakanin gwamnati da 'yan tawaye ka iya yaduwa a yankin.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta nuna damuwa akan rahotannin da ke nuna sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta a watan da ya gabata tsakanin gwamnatin Shugaba Salva Kiir da magoya bayan tsohon mataimakinsa Riek Machar.

Sai dai gwamnati ta musanta zargin da 'yan tawaye ke yi na cewa ta kawo mayakan Sudan da na Congo domin gujewa tsagaita wuta.

Magoya bayan tsohon Shugaban kasar Riek Machar sun yi artabu da sojojin gwamnati kafin a kai ga yarjejeniyar tsagaita wuta.

Karin bayani