Za a koma tattaunawa kan Sudan ta Kudu

Taron tattaunawar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Taron tattaunawar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

Za a ci gaba da zaman tattaunawar neman zaman lafiya a Ethiopia don kawo karshen tashe-tashen hankula da zub da jini a makwabciyarta Sudan ta Kudu.

Tashin hankalin da aka shafe kusan wata biyu ana yi yayi mummunan tasiri a jariyar kasar ta Sudan ta Kudu.

Ana dai zargin bangarorin biyu da ba sa ga maciji da juna da yin watsi da batun tsagaita wutar da suka amince a cikin watan da ya gabata.

Wata kungiya da ke lura da al'muran kasashen gabashin Afirka ta aike da tawagar masu sa ido zuwa Juba babban birnin kasar don tabbatar da ganin an tsagaita wutar.

Yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya ta kididdige cewa mutane fiye da milyan daya da rabi ne ke cikin matsanancin hali dake bukatar abinci a Sudan ta Kudun sakamakon tashin hankalin.