An karya yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption kai agaji ya sami tsaiko a Syria

Majalisar Dinki Duniya ta yi kira ga gwamnatin Syria da kuma 'yan tawaye da su martaba yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Homs.

Wannan kiran ya biyo bayan farma ma'aikatan agaji yayin da suke kokarin kai abinci da magunguna zuwa birnin da akayiwa kawanya.

Jami'ar bada agajin gaggawa ta Majalisar Dikin Duniya Valerie Amos ta ce taji matukar takaici kan sabawa yarjejeniyar tsagaita wutar da akayi na kwanaki uku.

Kakakin Kungiyar bada agaji ta Syria wato Syrian Red Crescent na cewa dole ne a bada tabbacin tsagaita wuta kafin aiyukan ceton ya ci gaba a birnin.

Karin bayani