Ƙunar Baƙin Wake: Dara ta ci gida a Iraq

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Jami'an gwamnatin Iraqi sun ce, dara ta ci gida yayin da wasu masu shirin ƙunar baƙin wake su ashirin da ɗaya suka mutu yayin da suke ƙoƙarin ƙullo bama-bamai na ƙunar baƙin wake.

Wani jami'n gwamnatin Iraqin yace, masu tsatsauran ra'ayin suna daukar Vidiyo ne da za'a bayyana bayan sun kai harin kunar bakin wake, sai bisa tsautsayi bama-baman da suka sanya a jikinsu suka tashi.

Cikin wannan shekarar dai an samu karuwar hare-haren kunar bakin wake da 'yan kungiyoyin dake da alaka da Al Qaeda, kuma koda cikin watan jiya an kashe mutane fiye da dubu a sassan Iraqi.

Iraq dai tana fama da tashin hankali na bangaranci tsakanin 'yan Shi'a da mabiya Sunni.