NAFDAC ta koka da magungunan jima'i

Hakkin mallakar hoto nafdac
Image caption Shugaban NAFDAC, Dr Paul Orhii

Hukumar NAFDAC mai kula da ingancin abinci da magunguna a Nigeria ta koka da yawan sayar da magugunan jima'i a arewacin kasar.

NAFDAC ta ce magungunan karfin maza da kuma na mata da akan yi wa lakabin "manta-uwa" ko kuma "gida-da- mota" na iya yin illa ga lafiyar al'umma.

Hukumar ta ce baya ga hade-haden gargajiya, yanzu haka kuma ana fasa-kwaurin ire-iren wadannan magunguna daga China ba tare da izini ba.

Sai dai kuma masu amfani da magungunan da dama na cewa su na da matukar muhimmanci wurin inganta zaman aure.