Dattawan Arewa sun rabu kan taron kasa

Tanko Yakasai
Image caption Tanko Yakasai, shugaban majalisar dattawan arewa, NEC.

Sabuwar kungiyar majalisar dattawan arewacin Nigeria, karkashin Alhaji Tanko Yakasai ta bayyana goyon bayanta ga taron tattauna makomar kasar da ake cece-kuce a kai.

Wasu kungiyoyin dattawan arewan irinsu Northern Elders Forum sun bayyana adawarsu da taron da su ka ce zai bi ra'ayin shugaban kasa ne kurum ganin yadda aka shirya nada mahalartansa.

Wakili a kungiyar ta Northern Elders Council Alhaji Isah Tafida Mafindi ya ce halartar 'yan arewa taron na da matukar muhimmanci saboda ita tafi kowanne bangare na Nigeria korafi kan yadda aka yi watsi da ita

Ya kuma musanta cewa su 'yan amshin shatar shugaba Goodluck Jonathan ne.

Sai dai kakakin Northern Elders Forum, Farfesa Ango Abdullahi ya ce taron ba zai amfanar da 'yan kasar ba, saboda za a bi tsarin da gwamnati take so ne kawai, saboda ita ce tafi yawan wakilai a taron.

Karin bayani