Ntaganda ya gurfana gaban kotun ICC

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bosco Ntaganda ya jagoranci dakarun 'yan tawaye

Tsohon madugun 'yan tawaye a Congo, Bosco Ntaganda ya gurfana gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya-ICC a Hague.

Ntaganda ya musanta zargin aikata laifukan yaki a gabashin jamhuriyar dimokradiyar Congo, shekaru 10 da suka wuce.

Bosco Ntaganda wanda a Congo ake kiransa 'The Terminator' shi ne mutum na farko da ya mika kansa ga kotun bisa tuhumar aikata laifukan yaki a kasar.

Ya mika kansa ne a ofishin jakadancin Amurka dake Rwanda a bara.

Mr Ntaganda na daga cikin wadanda kotun ICC ke nema ruwa a jallo, inda ake tuhumarsa kan laifuka 18 ciki har da amfani da kanannan 'yan mata a matsayin sojoji tare da yin lalata dasu.

Sai dai ya musanta baki dayan zarge-zargen da ake masa.

Karin bayani