'Yan tawaye ba zasu halarci tattaunawa ba

Hakkin mallakar hoto Getty AFP
Image caption Riek Machar, jagoran 'yan tawaye

'Yan tawayen Sudan ta kudu sun fitar da wata sanarwa dake cewa, zasu kauracewa zagaye na biyu na tattaunawar samar da zaman lafiya da aka shirya somawa yau a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

'Yan tawayen dai sun ce, ba zasu koma kan teburin shawara ba har sai an sako sauran wasu fursunonin siyasa hudu.

Sun kuma ce, ba zasu zauna domin tattaunawa ba har sai dakarun Uganda dake goyon bayan gwamnati sun janye daga kasar.

An shirya tattaunawar ce domin kawo karshen fadan da ya yi sadaniyyar mutuwar dubban mutane tun bayan shugaba Salva Kiir ya zargi jagoran 'yan tawaye kuma tsohon mataimakinsa, Riek Machar da kokarin yin juyin mulki.