China da Taiwan za su tattauna dangantakarsu

Tekunn yankin kudancin China Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tekunn yankin kudancin China

China da Taiwan za su yi wata muhimmiyar tattaunawa tun bayan kawo karshen yakin basasa da aka yi a shekarar 1949.

Ministan gwamnatin Taiwan mai kula da manufar China kan tsibirin zai gana da takwaransa na China a birnin Nanjing da ke gabashin kasar.

China dai ta na daukar Taiwan a matsayin wani lardi da ya balle daga cikinta, kuma a can baya ta bi hanyoyi da dama na sasantawa ta hanyar kungiyoyi.

Taiwan din dai ta ce tattaunawar da za a yi na da matukar muhimmanci ga karfafa dangantaka tsakanin bangarorin biyu.