Kokarin sulhu tsakanin China da Taiwan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption China na kallon Taiwan a matsayin wani yankinta

China da Taiwan sun ce za su karfafa dangantaka a tsakaninsu, bayan da gwamnatocin bangarorin biyu suka gana a karon farko tun bayan da 'yan Communist suka hau mulki a 1949.

Sun amince cewa, ma'aikatunsu za su rika tuntubar juna a kai a kai.

Ministan Taiwan dake kula da manufofin tsibirin Wang Yu-Chi ya bayyana tattaunawarsa da takwaransa na China Zhang Zhijun a matsayin wani sabon babin dangantakar bangarorin biyu.

China dai na daukar Taiwan a matsayin wani yankinta da ya balle.

A hukumance ba a bayyana abubuwan da za a tattauna ba a taron.

Karin bayani