An kara kai agaji Homs na Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fararen hula a birnin Homs

Wakilin BBC a birnin Homs na Syria ya ce motocin abinci biyu sun isa tsohon birnin da aka yi wa kofar raggo.

Haka kuma akwai motocin daukar fasinja da ke jiran fitar da fararen hula daga cikin birnin.

Wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin-gadi na kawo karshe ranar Laraba, sai dai gwamnan Homs ya shaida wa wakilinmu cewa zai yi kokarin kara wa'adinta har sai an kammala kwashe mabukata.

Kawo yanzu dai mutane 1,200 ne su ka bar Homs.

Magoya bayan gwamnati sun fusata bisa zargin za a iya barin 'yan bindiga su tsere daga birnin, yayin da 'yan adawa ke nuna rashin amincewa da tantacewar da ake yi wa matasan da ke barin Homs.

Karin bayani