Jonathan ya sallami ministoci hudu

Hakkin mallakar hoto fgn
Image caption An sha neman a kori ministar sufurin sama, Stella Oduah bayan da aka same ta da laifin sayen motoci kan N255m ba da izini ba.

Shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya sallami ministar sufurin jiragen sama, Ms Stella Oduah wacce ake zargi da badakalar sayen motoci ba bisa ka'ida ba.

Sauran ministocin da ya sallama sun hada da Caleb Olubolade na al'amuran 'yan sanda, Godsday Orubebe na ma'aikatar Niger Delta da Yerima Ngama, minista a ma'aikatar kudi.

A baya dai an sha kiraye-kirayen Mr Jonathan ya sallami Stella Oduah saboda sayen motoci biyu masu sulke kan farashin Naira miliyan 255, ba tare da amincewa ba.

Kawo yanzu fadar shugaban kasa ba ta baiyana dalilin sauke su ba.

A Larabar nan dai majalisar dattawan Nigeria ta fara tantance mutanen da shugaba Jonathan ke neman nada wa sababbin ministoci.

Karin bayani