David Mark ya dakile yinkurin sanatocin APC

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Akwai rarrabuwa kawuna tsakanin sanatoci kan matakin Sanata David Mark

Shugaban majalisar dattijan Nigeria, David Mark ya kara dakile yinkurin wasu sanatoci 11 daga ficewa a jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

A cewar shugaban majalisar ba za a amince da komawarsu ba har sai an warware takkadama kan batun a kotu.

Jam'iyyar PDP ta shigar da kara gaban kotu ne inda take neman kwace kujerun sanatoci saboda kokarin hadewa da 'yan adawa.

Sai dai sanatocin sun ce PDP ba tada hurumin kwace musu kujerun.

'Raunin PDP'

Tun a ranar 29 ga watan Junairu sanatocin suka bayyana sauya sheka daga PDP zuwa APC, amma kuma shugaban majalisar, David Mark yaki sanar da sauya shekar a zauren majalisar.

Sanatoci da suka sauya shekar su ne Bukola Saraki da Shaba Lafiagi da Mohammed Ndume da Danjuma Goje da Abdullahi Adamu da Magnus Abe da kuma Wilson Ake.

Sauran sune Bindo Jubrilla da Abdullahi Gobir da kuma Alhassan Aisha Jummai.

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan wanda shi ne jagoran jam'iyyar PDP na fuskantar koma baya saboda matsin lamba daga wasu 'ya'yan jam'iyyar tare da kuma sauya shekar da wasu jiga-jigan PDP suka yi zuwa APC.

Tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Alhaji Atiku Abubakar da wasu gwamnoni biyar sun bar PDP sun koma APC.

Karin bayani