Sakacin iyaye na jefa yara cikin hadari

Image caption Wasu yara na wasanni da wayoyin zamani

Yawancin iyaye basu san hadarin da 'ya'yansu za su iya fuskanta ba sakamakon amfani da wayoyin komai da ruwanka irinsu iPhone.

Wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewar yaro daya cikin biyar ya ce ya saka wasu manhajoji a cikin wayarsa da iyayensa basu san dasu ba.

Wani bincike na daban, ya nuna cewar kashi 20 cikin 100 na iyaye basa sa ido kan abubuwan da 'ya'yansu ke yi a shafukan intanet.

Kashi 90 cikin 100 na wasu iyayen da BBC ta bincika a Ingila sun bayyana cewar basa lura da abubuwan da 'ya'yansu ke yi a kan shafukan intanet.

A halin yanzu dai kamfanin Apple mai kera wayar iPhone da kuma iPad yana da tsarin hana yara shiga shafukan da basu dace ba har sai an saka lambobin makullin shiga shafin.

Haka kuma wayoyi masu amfani da manhajar android suma suna da abubuwan kariya daga shiga shafukan batsa.