Sudan ta Kudu: An soma tattaunawar sulhu

Hakkin mallakar hoto Reuters

An soma zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Sudan ta kudu da 'yan tawaye.

An kammala zagayen farko na tattaunawar ce yayin da aka zagaita wuta a karshen watan Janairu.

Sai dai kuma dukkan bangarorin biyu sun zargi juna da keta yarjejeniyar tsagaita wutar.

Su dai 'yan tawaye sun ce, janyewar dakarun Uganda na daga cikin sharrudan sasantawa tsakanin gwamnati da 'yan tawayen.

Sai dai gwamnati ta ce, dakarun Uganda basa fada da kowa.