Za a kara kai agaji birnin Homs na Syria

Masu rabon agajin abinci a Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rabon agajin abinci a Syria

Ma'aikatan agaji a kasar Syria su na shirin kai karin wasu kayan abinci da magunguna ranar Talata ga mazauna birnin Homs bayan an kara tsawon wa'adin tsagaita wuta da kwanaki uku.

Ana kuma fatar kwashe karin wasu mutanen dake neman dauki.

An dai kwashe Mata da Yara da gajiyayyu sama da 1,000 daga cikin birnin a yarjejeniyar farko da aka kulla.

Za a kuma ci gaba da tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan tawaye a yayinda masu shiga tsakani na kasa-da-kasa ke kokarin neman amincewarsu ga shirin kai kayan agaji ga mutane kimanin 250,000 da aka yi wa kofar-raggo a wasu yankuna na kasar.

Tattaunawar kuma har ila yau tana kokarin lalubo hanyoyin dakatar da rikicin da kuma kafa gwamnatin rikon-kwarya.

Karin bayani