CAR: Amnesty ta caccaki dakarun Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministan tsarn Faransa Yves-Le-Drian na ziyara a Bangui

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce, a jamhuriyar tsakiyar Afirka, mayakan sa-kai Krista na kaiwa al'ummar Musulmi hare-hare da zummar kawar da su kwata-kwata.

Tun farko a yau wata kungiyar kare hakkin dan adam din, Amnesty International, ta ce, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasashe sun kasa hana abinda ta kira: kisan kare dangi a kan Musulmi, a yammacin kasar.

A cikin rahoton da ta fitar, Amnesty ta ce, sojojin Faransa da na Afirka da ke kasar, ba sa wata hobbasa wajen kalubalantar mayakan sa-kan Anti-Balaka da galibi Kirista ne, wadanda ke kaiwa Musulmi hare-hare.

A bangare daya kuma, hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ta ce, jirgin farko dake dauke da kayan abinci da ake matukar bukata ya isa Bangui, babban birnin kasar.

Kashin na farko dai shinkafa ce tan tamanin da biyu da aka shigar kasar daga Kamaru.

Nan da wata guda dake tafe dai hukumar tana fatan ciyar da mutane dubu dari da hamsin.

Sai dai kuma kiyasi na nuna cewa, mutane fiye da miliyan guda ne ke matukar bukatar agajin abinci a kasar.

Karin bayani