Ba mu bai wa 'yan majalisa kudi ba — PDP

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption PDP ta ce APC ta kusa wargajewa shi ya sa take kame-kame

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta musanta cewa ta bai wa 'yan majalisar tarayyar kasar makudan kudade domin su sake komawa cikinta.

Jam'iyyar APC ce dai ta yi zargin bayan 'yan majalisa biyar sun fice daga cikinta zuwa PDP ranar Talata.

PDP ta ce 'yan Nigeria na gari sun damu da ire-iren kalaman da APC take yi wadanda, a cewarta, ke da nufin yin kafar-ungulu ga mulkin dimokaradiyya da kuma jefa kasar cikin rikici.

Ta kara da cewa APC ta fara wargajewa ne shi ya sa take kame-kame.

Karin bayani