Cocin Nigeria na yaduwa a Amurka

Image caption Fasto James Fadele, jagoran RCCG a arewacin Amurka.

A shekarun baya Turawan Mishan ne ke zuwa Afrika domin yada addinin Kirista. Sai dai yanzu lamarin ya sauya salo, inda wani coci a Nigeria ke fatan bude rassa a Amurka wanda yawansu ya kai shagon sayar da gahwa na Starbucks.

Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) wanda aka kafa a Nigeria a 1952 na gina wani katafaren dakin taro mai cin mutane 10,000 a wani kauye da ke arewa da Dallas, a jihar Texas ta Amurka.

Cocin na daga cikin wadanda su ka fi yawan mabiya a Afrika, inda ya ce ya na da mabiya fiye da miliyan biyar, mafi yawansu a Nigeria.

Fasto James Fadele, wanda ke shugabantar cocin a nahiyar arewacin Amurka, ya ce Ubangiji ne ya yi wa jagoran cocin na duniya Enoch Adeboye wahamin cewa zai kafa cibiyarsa ta arewacin Amurka a kusa da birnin Dallas.

Burin Fadele shi ne ya kafa reshen cocin RCCG a nisan kilomita goma-goma a fadin nahiyar domin kai mutane da dama cikin aljanna.

Kaso 20% na kudin shiga

Ya ce; "Saboda aljanna gaskiya ce, kuma Ubangiji gaskiya ne, shi ya sa muke son bude rassan coci da adadinsu ya kai yawan kantunan Starbucks.

Shugabannin RCCG sun ce su na da rassa 720 arewacin Amurka, abinda ya nunka adadin rassan na shekaru hudu da su ka wuce, kuma sun ce su na da mabiya 15,000 a kasar Amurka.

Ruth Marshall ta jami'ar Toronto, wacce ke nazari kan coci-cocin Afrika ta ce rassan RCCG na matukar karuwa ne sakamakon matsi daga jagoran cocin Enoch Adeboye a Nigeria.

Ta ce; "Ya na matukar so ya ga ana dama wa da shi a duniya. Kuma za a iya cewa ya matsu ya ga rassansa sun karu saboda wannan shi ne alamar nasararsa. Haka kuma, karuwar rassan na haifar da karin kudin shiga ga cibiyar cocin da ke Nigeria."

Ta ce kowanne fasto na aika kaso 20% na kudin shigar da reshensa ya samu zuwa ga cibiyarsa da ke Nigeria.

Image caption Mabiya RCCG a Amurka 'yan asalin Afrika ne ba Amurkawa ba.

Sai dai kuma mafi yawan masu ibada a cocin RCCG 'yan Afrika ne da ke zuwa domin tuna gida, kuma idan har cocin ya na son cika burinsa na zama kamar Starbucks a Amurka sai ya jawo hankalin turawa sun fara bauta a cikinsa.

Wannan ne kuma da kamar wuya, domin kuwa ko 'ya'yan da 'yan Afrika ke haifa a Amurka sun fi son zuwa wasu cocin da su ka dace da dabi'unsu sabanin RCCG inda ake warkar da mara sa lafiya ta hanyar addu'o'i da wake-wake.

Sai dai hakan bai karya gwiwar fasto James Fadele da ke Texas ba.

Ya ce; "Idan mutane su ka gane da gaske mu ke, za su shiga cocinmu."