Syria: Kayayyakin abinci sun isa Homs

Image caption An kwashe daruruwan mutane daga birnin

Masu aikin agaji a Syria sun koma ayyukan ceto a garin Homs bayan da suka dakatar da kwana guda.

Gwamnan Homs ya ce an kwashe mutane fiye da 200 wadanda a baya suka makale sakamakon rikicin.

A ranar Laraba yarjejeniyar tsagaita wuta za ta zo karshe, amma gwamnan birnin Homs din ya ce, zai iya kokarin tabbatar da cewa, tsagaita wutar ta dore.

Kakakin hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya, Dina Elkassaby ta ce, wadanda suka rage a birnin Homs suna matukar bukatar daukin gaggawa.

A daya bangaren kuma masu fafutuka a Syria sun ce, jiragen saman yaki na sojan gwamnati suna ta kai hari a garin Yabroud dake kusa da kan iyaka da Lebanon.

Hotunan bidiyo da aka sanya a kafar sadarwa ta Intanet sun nuna wasu abubuwa suna fashewa, kuma hayaki ya turnuke samaniyar garin na Yabroud, wanda shi ne gari na karshe 'yan tawaye suke iko da shi a yankin Qalamoun mai tsaunuka akan iyaka.

Karin bayani