Magajin garin New Orleans ya ci hanci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ray Nagin, ya musanta laifinsa kuma ya ce zai daukaka kara

An samu magajin garin New Orleans na Amurka a lokacin da mahaukaciyar guguwar Katrina ta yi barna a 2005 da laifin cin hanci da rashawa tare da kin biyan haraji a zamanin mulkinsa.

Wata kotun tarayyar Amurka ce ta samu Ray Nagin da laifin karbar cin hancin da ya kai dubunnan daruruwan daloli daga hannun 'yan kwangila domin taimakawa a ba su aikin sake gine-ginen New Orleans da mahaukaciyar guguwar ta lalata.

Mr Nagin na fuskantar akalla shekaru 20 a gidan yari.

Sai dai tsohon magajin garin ya musanta laifinsa, inda ya ce hakika zai daukaka kara.