Yaki da haramtaccen cinikin namun daji

Cinikin hauren gwiwa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Giwaye na fuskantar barazana saboda haurensu

Wani rukunin kasashe 46 dake halartar wani taron kasa da kasa kan haramtaccen cinikin namun daji da ake yi a London, sun yi alkawarin daukan kwararan matakai na yaki da farautar dabbobin daji.

An dai kiyasata cewa haramtaccen cinikin dabbobin daji, yana samar da dala biliyan 19 a shekara ga mafarauta.

Hakazalika wasu shugabanin kasashe hudu na Afirka sun yi alkawarin goyon bayan wani kuduri dake haramta sayar da hauren giwa har tsawon shekaru goma, a wani yunkuri na kare giwaye.

Shugabanin wadanda suka hada da na Botswana da Gabon da Chadi da kuma na Tanzania .

Tun farko wasu kwararru kan kare gandun daji sun shaidawa taron cewa cin hanci da rashawa yana taimakawa wajen fitar da kwantenoni cike da hauren giwar daga nahiyar Afirka.

Karin bayani