Amurka ta yi tur da hari a garin Konduga

Image caption Mata 'yan makaranta a jihar Borno na fuskantar barazanar sata daga 'yan bindiga.

Gwamnatin Amurka ta yi Allah wadai da harin da aka kai a garin Konduga na jihar Borno inda aka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu.

Amurkan ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa daga ofishin jakadancinta da ke Abuja.

Amurkan ta kuma bayyana matukar damuwa dangane da batun sace wasu 'yan mata da maharan suka yi a wata makarantar sakandiren 'yan mata da ke garin Konduga ranar 11 ga Fabrairu.

Sai dai gwamnatin jihar Borno ta ce binciken da ta ya zuwa yanzu, bai kai ga tabbatar da cewa an yi awon gaba da 'yan matan ba a lokacin harin.

Kimanin mutane 40 ne dai 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne su ka kashe yayin harin tare da jikkata wasu da dama.

Karin bayani