Facebook ya kawo tsarin zabar jinsi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A bisa sabon tsarin mutum yana da damar sakaya jinsinsa

Shafin sada zumunta na Facebook ya bullo da tsarin da masu mu'amala da shi musamman 'yan luwadi da madigo da wadanda su ka sauya jinsi za su iya zabar jinsin da ya dace da su.

Bayan zabin mace ko namiji , shafin ya kuma samar da wasu zabin daban-daban kusan 50 da mutane za su iya zaba domin nuna irin jinsinsu.

Haka kuma shafin ya samar da wakilin suna na shi ko ita ko su.

Kamfanin Facebook ya ce yi aiki ne tare da kungiyoyin 'yan luwadi da madugo da masu sauya jinsi wajen fitar da sabon tsarin.

Sai dai kuma masu gudanar da shafin ba su bayyana lokacin da masu amfani da shafin da ke wajen Amurka za su fara cin moriyar sabon tsarin ba.