An amince da murabus din Firaministan Italiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Enrico Letta

Shugaban Italiya, Giorgio Napolitano ya amince da murabus din Firayiministan kasar Enrico Letta.

Mr Letta dai ya mika takardar murabus dinsa kwana daya bayan jam'iyyarsa ta Democratic ta kada kuri'ar janye goyon bayanta ga gwamnatinsa ta hadin guiwa.

Mai yiwuwa Shugaba Napolitano ya nemi shugaban jam'iyyar da aka zaba kwanan nan, Matteo Renzi da ya kafa wata sabuwar gwamnati.

Mr Renzi, mai shekaru 39 a duniya, ya sha nanata kiran tsaffin 'yan siyasa su san inda dare yayi masu su bar sabbin jini su zaburar da tattalin arzikin kasar.

Amma kuma shi ne magajin garin Florence, ba zababben dan majalisar dokoki ba ne ba.

Karin bayani