" 'Yan sanda na cin ribar fyade a Kano"

Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Sufeto Janar Muhammad Dahiru Abubakar.

Iyayen wasu kanan yara uku da aka yi wa fyade a jihar Kano da ke arewacin Nigeria sun zargi jami'an 'yan sanda da neman cin hancin N5,000 daga wajensu domin taimaka mu su a wajen shari'a.

Iyayen dai sun ce tun farko sai da aka karbi N1,000 daga wajensu a matsayin kudin bude fayil.

To sai dai runduar 'yan sandan ta ce tuni ta fara daukar matakin ladabtar da wadanda ake zargin, idan har zargin ya tabbata.

Matsalar fyade dai matsala ce da hukumomi ke cewa na kara yawaita a kasar.

Karin bayani