Masu wasikar soyayya na sharafi a Mali

Image caption Alassane Maiga (dama) da wani abokin cinikinsa.

A yayin da ake ci gaba da harkokin makon masoya a fadin duniya, masu rubuta wasikar soyayya a Bamako, babban birnin Mali kakarsu ta yanke saka.

Alassane Maiga na daya daga cikin masu rubuta wasika 10 da ke zama a kofar babban gidan waya na Mali.

A kasar da kaso 70% na al'ummarta ba su iya karatu da rubutu ba, sana'ar marubutan ita ce cike fama-famai da kuma tsara wasiku masu dauke da dadadan kalamai masu narka zuciyar masoya.

Amma wannan makon shi ne kakar su Alassane da takwarorinsa inda su kan yini su kwana su na ta zakulo kalaman soyayyar da su ke rattaba wa a wasikun da suke rattaba wa jama'a har sai barci ya kwace musu a kofar gidan wayar.

Kure adaka

Baya ga dimbin wasikun da su ke rubutawa, kure adakar su Alassane shi ne rubutacciyar wakar soyayya. Farashinta dai ya kan kai N650; watau nunkin farashin wasika sau hudu.

Rubuta wasikar soyyaya dai ba abu ne da ake yin sa kara zube ba. Alassane kan binciki yanayi da kuma karfin soyayyar da ke tsakanin mai sakon da kuma rabin ransa.

Hakan kuma ya kan binciki manufar wasikar; tsari, birgewa, nishadantarwa ko kuwa shawo kai? Ko kuma ma akwai bukatar neman afuwa bayan samun sabani? Wacce za a aike wa wasikar kawa ce ko kuma budurwa?

Bugu da kari ya kan yi nazari akan mai aikewa da sakon; gaye ne ko kuma gaja?

"Mu kan sa kanmu a matsayinsu domin isar da sakon da zai gamsar da masoyansu." in ji Alassane.

Ya kuma amince cewa ga wasu takwarorin aikinsa, rubuta wasika hanyar cin abinci ce kawai. Amma bayan shekaru 15 ya na wannan sana'ar, ya kan dauki aikinsa na mai shiga tsakani da matukar muhimmanci.

"Manufata" a cewarsa "ita ce taimakawa mutane."