Pistorius na alhinin kashe budurwarsa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pistorius ya harbe Steenkamp a gidansa a bara.

Zakaran tseren Olympics na nakasassu dan Afrika ta Kudu, Oscar Pistorius ya bayyana "alhini" game da harbe budurwarsa Reeva Steenkamp, shekara guda bayan rasuwarta.

Sanarwar da ya fitar ta bayyana harbin budurwa a matsayin "mummunan tsautsayi."

A watan gobe ne dai zai gurfana gaban kotu bisa tuhumar kisanta.

Ya ce ya harbe ta a gidansa ne saboda ya yi zaton barawo ne.

Sai dai masu shigar da kara sun ce da gangan ya kashe ta bayan da su ka samu sabani.