'Yan bindiga sun kai hari kusa da Baga

Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a kusa da garin Baga, dake jihar Bornon Najeriya.

Sun kai harin ne ran Juma'a da daddare a wani wurin da ake kira Madaye Doron Baga, wanda ke kusa da kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Chadi.

Mazauna wurin sun ce an kashe mutane a harin, wasu da dama kuma sun tsere zuwa kasar Chadi.

Wani daga cikin wadanda suka tseren, wanda ba ya son a ambaci sunanshi domin fargabar abinda ka iya biyo baya, ya ce har yanzu suna can sun boye a cikin daji.

Ya ce wandanda suka kai harin sun je da manya bindigogi, suna kabbara. Ya kuma yi ikirarin cewa 'yan bindigar sun fafata da sojojin dake sintiri a wajen, amma sojojin sun tsere.

Da aka tuntubi kakakin runduna ta bakwai ta sojojin Najeriyar mai hedkwata a birnin Maiduguri, Kanar Muhammad Dole, don jin cikakken bayani akan lamarin, sai yace rundunar ba ta samu rahoton batun ba.

Kanar Dole ya ce shiyyar Baga tana karkashin ikon rundunar hadin gwiwa ta kasashen yankin ne, kuma ba su sanar da rundunar ta bakwai halin da ake ciki ba tukuna.

Yankin Bagar dai na daga cikin sassan da suka fuskanci hari mafi muni a hare-haren da masu tayar da kayar baya ke kaiwa a Jihar Borno.

Karin bayani