An dage shara'ar Morsi

Hakkin mallakar hoto AP

Hambararren shugaban Masar, Mohammed Morsi da wasu 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi sun gurfana a gaban wata kotu a birnin Al-kahira a bisa tuhumar leken asirin kasa.

Lauyoyin su sun fice daga kotun cikin fushi saboda an saka su cikin wani kejin ihunka banza.

Ana zargin su ne da hada kai da kungiyar Hamas ta Falastinu; da kungiyar Hezbollah ta Lebanon da kuma Iran.

An dage sauraron kakar.

Karin bayani