''Ba mu yaudari Sakkwatawa ba''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Goodluck ya yi alkawarin ba 'yan kasuwar tallafin Naira miliyan 250

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce babu yaudara kan alkawarin da ta yi na tallafa wa wadanda masifar gobara ta auka wa a kasuwar Kara ta Sokoto.

Shugaban Najeriyar ne dai ya yi wannan alkawarin lokacin da ya je bikin karbar tsohon gwamnan jihar Alhaji Dalhatu Attahiru Bafarawa da ya sauya sheka daga APC zuwa PDP tattalafin da 'yan adawa suka ce na siyasa ne.

Mataimakin gwamnan jihar ta Sokoto Alhaji Mukhtari Shagari ya shaida wa wakilinmu a wata tattaunawa cewa tuni gwamnatin tarayyar ta yunkuro don cika wannan alkawari.