Obama na ganawa da sarkin Jordan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mr Obama ya nuna cewa yana sake tunani kan manufarsa game da Syria.

Shugaba Obama na ganawa da sarki Abdullah na Jordan, a tattauwar farko cikin jerin ganawar da zai yi da kawayen Amurka na yankin Gabas ta Tsakiya domin kara tabbatar musu da goyon bayan Amurka.

A dukkanin ganawar da zai yi da jagororin kasashen, zai tattauna batun Syria da yarjejeniyar nukiliyar Iran da kuma batun shirin zaman lafiyar Gabas ta Tsakiyan.

Shugaba Obaman zai gana da Fraiministan Israela, Benjamin Netanyahu a sati biyu masu zuwa sannun kuma ya je Saudi Arabia a karshen watan Maris.

Kawayen Amurka a yankin na Gabas ta Tsakiya dai na nuna damuwa cewa Amurka na hanzarin kulla yarjejeniya da Iran.