Yau za ayi tattaunawa ta karshe kan Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Brahimi zai gana ta karshe da Syria da 'yan tawaye

Jakadan musamman na Majalisai Dinkin Duniya a rikicin Syria zai yi tattaunawa ta karshe da bangarorin da ke yaki da junansu a Geneva a yau Asabar, domin dorewar tattaunawar zaman lafiyar.

Babu wani ci gaba da aka samu dai a zagaye na biyu na tattaunawar abin da har ya sa jakadan Lakhdar Brahimi ya furta cewa suna fuskantar hadarin rashin nasara.

Masu lura da al'amura dai na ganin babbar nasarar da Majalisar Dinkin Duniya za ta iya samu a yanzu ita ce, bangarorin da ke rikicin su amince da dawowa wani zagayen zaman tattaunawar.

Zagayen farko na tatataunawar dai da aka yi a watan Janairu ya haifar da 'yar kwarya kwaryar yarjejeniyar amin cewa a kai agaji ga alummar birnin Homs da kuma kwashe farar hula.

Karin bayani