An zargi Syria da rusa tattaunawa a Geneva

Image caption Ba a sami nasara ba a tattaunawar Geneva ba

Kasashen Faransa da na Birtaniya sun zargi gwamnatin Syria da rusa tattaunawar zaman lafiya da 'yan adawa a Geneva.

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce jami'an gwamnatin Shugaba Assad sun toshe duk wata kafa da za a iya kafa gwamnatin rikon kwarya.

Wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Syria Lakhdar Brahimi neman afuwa ya yi ga 'yan Syria ya ce bai iya sa wata rana don ci gaba da tattaunawar ba amma dai suna fatan za a ci gaba a wani lokaci.

Sakataren harkokin waje na Birtaniya William Hague, ya zargi gwamnatin Syria da rusa tattaunawar ta wanzar da zaman lafiya.

Karin bayani