Boko Haram: An kashe mutane 106 a Izge

Kungiyar Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yiwa wasu mutane yankan rago a garin Izge

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a Najeriya sun kashe mutane sama da 100 a garin Izge na jihar Borno.

An yi janaizar fiye da mutum 60 da aka kashe a harin na ranar asabar da daddare.

Wadanda suka tsira a harin sun ce maharan sun tara mutane kamar 30 kana suka bude masu wuta

Daga bisani kuma suka yi ta bi gida-gida suna harbe mutane, yayin da suka yi wa wasu da dama yankan rago.

Yanzu haka dai dubban mazauna garin ne suka tsere zuwa Karamar Hukumar Madagali ta Jihar Adamawa.

Karin bayani