Satar bayanai :Turai za ta sake dabara

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Angela Merkel na ganin matakin zai magance satar bayanan sadarwa

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta tuntubi Faransa kan kirkiro matattarar sadarwa ta kasashen Turai domin hana wasikun e-mail da sauran bayanai na intanet ratsawa ta Amurka.

Uwargida Merkel ta ce za ta bijiro da batun domin tattaunawa da shugaba Francois Hollande lokacin ziyarar da za ta kai Paris a makon da za a shiga.

Batun satar tattara bayanai na tarho da sauran sadarwa da suka hada da satar suraron wayar tarhon shugabar gwamnatin Jamus din da Hukumar Tsaron Amurka ta yi ya sanya damuwa a Turai.