Ana korafin nada mikamai a Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Guguwar siyasa na kadawa a Gombe

A jihar Gomben Najeriya ana cece-ku-ce kan nada mashawarta da mataimaka na musamman ga gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo.

Gwamnatin dake arewa maso gabashin kasar ta bai wa karin mutane kimanin tamanin mukaman, baya ga wasu fiye da dari hudu da aka bawa mukaman a 'yan kwanakin baya daga yankuna daban-daban na jihar.

Wasu dai na ganin nada daruruwan mukarrabai tamkar barnar dukiyar jama'a ce domin yadda akan kashe kudade masu yawa wajen biyan albashi da alawus alawus na jami'an gwamnatin.

'Yan adawa kuma na cewa akwai ma alamar yaudarar jama'ar jihar Gombe a matakin da gwamnatin ta dauka.

To sai dai gwamnatin jihar ta Gombe ta ce ta yi nadin ne domin mutanen su bayar da gudummawarsu ga ci gaban jihar.

Karin bayani