'Sojan Nijeriya ba su da kayan aiki'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kashim Shettima, gwamnan jihar Borno

Gwamnan jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya, Kashim Shettima ya ce, rashin kayan aiki ne yasa har yanzu aka kasa kawo karshen kashe-kashen jama'a da kungiyar Boko Haram take yi.

A wata hira da BBC gwamnan ya kuma ce, makaman da kungiyar Boko Haram suke amfani da su sun fi karfin na sojan Najeriya.

Gwamna Shettima ya kuma ce, idan har aka samar da kayan aiki sosai dakarun Najeriya zasu iya kawo karshen rikicin Boko Haram.

A karshen makon da ya gabata ne dai 'yan kungiyar Boko Haram suka hallaka mutane fiye da dari a kauyen Izge na jihar ta Borno.

Jihar Borno ita ce tafi fama da hare-haren 'yan kungiyar ta Boko Haram.