An tilastawa jirgin Ethiopia sauka a Geneva

Jirgin Habasha a Geneva
Image caption An kwace jirgin Habasha tare da tilasta masa sauka a Geneva

An tsare wani mai taimakawa matukin jirgin Kasar Habasha wanda ya taso daga Addis Ababa zuwa birnin Rome bayan da ya kwace jirgin tare da tilastawa masa sauka a birnin Geneva.

'Yan sandan Swiss sunce mai taimakawa matukin jirgin ya kwace tukin jirgin yayinda matukin jirgin yake hutawa.

An bada rahotan cewa ya nemi a bashi mafakar siyasa a can.

Mai taimakawa matukin jirgin dai ya mika kansa ne bayanda ya hau kan wata taga akan wata igiya.

Dukkanin Fasinjojin cikin jirgin dai da kuma ma'aikatansa sun tsira.

Mutane kusan 200 ne a cikin jirgin

Karin bayani