Firaministan mafi kuruciya a Italiya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sabon firaministan Italiya, Matteo Renzi

Mutumin da shugaban kasar Italiya ya zaba, domin zama praministan Italiya mafi kuruciya, Matteo Renzi na ci gaba da bayyana irin matakan da yake son dauka na aiwatar da sauye-sauye.

Mr Renzi mai shekaru 39, wanda kuma bai taba zama dan majalisar dokoki ba, yayi alkawarin daukar duk matakan ad su,a dace wajen sauya kundin tsarin mulkin kasar Italiya, da batun da ya shafi samar da guraben ayyukan yi da harkar ilmi da kuma ta tsarin haraji.

Jam'iyyarsu Matteo Renzi ba ta da rinjaye a majalisar dokokin kasar domin kafa sabuwar gwamnati a don haka sai ya bukaci hadin kan 'yan adawa don kafa gwamnatin ganbiza.

Masu aiko da labarai sun ce 'yan Italiya basu gamsu da kamun ludayin 'yan siyasa ba, abinda ya baiwa Mr Renzi farin jini a tsakanin al'umma.

Karin bayani