'Jonathan na kamun kafa wajen sarakuna'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ziyarar Jonathan Masarautu na jan hankula

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya ce ziyarar da ya kai wa wasu manyan sarakuna uku na kasar ba ta da alaka da siyasa ko kuma batun neman tsayawa takararsa shugabancin kasar a shekarar 2015.

A karshen makon daya gabata ne dai shugaban kasar ya ziyarci Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da Alaafin na Oyo Oba Lamidi Oyiwola Adeyemi na uku, da kuma Ooni na Ife Oba Okunade Sijiwade.

Kawo yanzu dai mukarraban shugaban kasar ba su bayyana takamaiman batutuwan da shugaba Jonathan din ya tattauna da sarakunan ba, lamarin da ya sa wasu 'yan kasar danganta ziyarar da siyasa.

An zargi shugaban kasar Good luck Jonathan da neman goyon bayan masarautun kasar don neman tsayawarsa takara.

Sai dai mai ba wa shugaban Najeriyar shawara ta fuskar siyasa Barrister Ahmed Gulak ya musanta haka.

Karin bayani