An kai hari a gidan Hamma Amadou a Yamai

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Alhaji Hamma Amadou, Shugaban majalisar dokokin Nijar

'Yan sanda a Jamhuriyar Nijar na budanar da bincike a gidan shugaban majalisar dokokin kasar, Alhaji Hamma Amadou bayan wani hari a aka kai a gidan sa dake Yamai.

Wasu 'yan bindiga ne suka hari gidan nasa a daren ranar Lahadi kuma har sun yi harbi a cikin gidan, duk da cewar babu wanda ya rasu sakamakon hari

Shugaban majalisar dokokin na Nijar, Hamma Amadun baya gida lokacinda aka kai harin.

Jami'yyarsa ta MODEM Lumana ta yi Allah wadai da harin.

Kawo yanzu dai gwamnatin Nijar ba ta ce komai game da harin.

Karin bayani