Obama ya gargadi Uganda kan dokar luwadi

Image caption Kudirin dokar hana luwadi a Uganda ya tanadi hukunci me tsanani

Shugaba Obama ya gargadi takwaransa na Uganda,Yoweri Musuveni da cewa idan har ya kuskura ya yi dokar hana luwadi da madugo dangantaka za ta yi tsami tsakaninsa da Amurka.

A bisa tanadin dokar da Ugandan ke neman kafawa , duk wanda aka kama da laifin aikata luwadi za a yanke masa hukunci me tsanani da ya hada da daurin rai da rai.

Mr Obama ya ce wannan doka za ta zama koma baya ga dukkanin 'yan kasar ta Uganda, kuma za ta bata sunan kasar ta fannin kare 'yancin dan adam na 'yan kasar.