Hezbollah za ta ci gaba da yaki a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nasrallah ya zargi Saudi Arabia da munafurci

Jagoran kungiyar Hezbollah ta 'yan Shia a Lebanon Hassan Nasrallah ya ce, 'yan kungiyarsa za su cigaba da yaki tare da dakarun gwamnati Syria.

A wani jawabi da ya yi ta talabijin, ya ce jerin munanan hare haren bam da ake danawa a mota da ake kaiwa a Lebanon na daga yakin da suke fafatawa a Syrian.

Nasrallah ya ce manufarsu ita ce hana 'yan gwagwarmayar Sunni masu tsattsauran ra'ayi da ke da nasaba da al-Qaeda kama kasar.

Hassan Nasrallah ya kuma zargi kasar Saudia da sauran kasashe da ke marawa 'yan tawayen Syria baya da munafurci.