Tafkuna na kafewa a Nijar

Wata Manomiya a Jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto b
Image caption Tafkin Tande dai ya kafe ba bu ruwa sam a cikinsa, abinda ke janyowa manoman rani na yankin rashin kwanciyar hankali inda baki daya amfanin noman su ya kone saboda rashin ban ruwa.

A Jamhuriyar Nijar, wata matsala da ake fuskanta a yankin arewa na jahar Damagaram itace ta kafewar tabkuna.

Manoma da makiyaya dake noman rani a yankin dai na cikin wani yanayi na zullumi sakamakon lalacewar kayan lambun da suka shuka.

Tafkunan da ke karamar hukumar Tanus din Damagaram da suka hada da tafkin Tande wanda masu aikin Garake ke cin gajiyarsa shekaru aru-aru da suka gabata ya kafe kaf babu ruwa a cikinsa.

Kayan lambun da aka shuka a yankin da abin ya shafa dai baki daya sun kone kurmus saboda rashin ban ruwa.

Manoman sun ce tun kafin tafkin ya kafe suka kaiwa hukumomin kasar kokensu akan a duba lamarin, sai dai shiru ka ke ji ba amo ba labarin gyaran sa.

Karin bayani