'Koriya ta Arewa na cin zarafin bil adama'

Kim Jong Un Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Koriya ta Arewa na fuskantar wahalhalu daga Mahukunta

Wani kwamitin majalisar dinkin duniya ya zargi Koriya ta Arewa da aikata laifuka akan bil adama kuma ya gargadi shugaban Kasar Kim Jong Un a wata wasikar da aka aike masa da cewa zai dau alhakin ta'asar da ake aikatawa.

Masu binciken majalisar dinkin duniyar sunce manyan Shugabannin Kasar zasu fuskanci shari'a saboda laifin azabtarwa da kashe kashen bil adama da ka iya kaiwa ga kisan kare dangi.

Tuni dai Koriya ta Arewa tayi watsi da rahotan, tana mai bayyana shi da cewa wata kutungwilar siyasa ce da Amurka da kawayenta ke shiryawa.

Ta kuma musanta cewa ana cin zarafin bil adama a Kasar.

China tace tana adawa da matakin da aka dauka akan Koriya ta Arewa a kotun manyan laifuka ta duniya, tana mai nuna alamun cewa zata hau kujerar naki ga duk wani mataki irinsa a kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya

Karin bayani