Izge: Mutane 10,000 sun tsallaka Adamawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram na kona gidaje da masallatai

Rahotannin da ke fitowa daga Jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin Nigeria na nuna cewar mutane sama da 10,000 ne suka tsallaka zuwa makwabciyar jihar wato Adamawa sakamakon harin da 'yan Boko Haram suka kai a kauyen Izge.

Mutane kusan 106 ne aka kashe a sakamakon harin na kauyen Izge dake karamar hukumar Gwoza.

Wadanda suka tallaka din sun nemi mafaka ne a karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawan.

Hukumar bada agajin gaggawa a Nigeria, NEMA ta ce kawo yanzu bata riga ta isa garin ba domin soma tallafawa mutanen.

Gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya yi alkawarin taimakawa mutanen suka yi asarar muhallinsu a kauyen na Izge.

Ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar dinkin duniya ya yi Allawadai da harin na Izge dama wanda aka kai a jihar Adamawa a kwanakin baya.

Wata sanarwa daga ofishin, ta ce harin ya jijjiggasu kuma ta yi kira ga gwamnati ta dauki matakan kare rayukan jama'a da dukiyoyin su.

Karin bayani